Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Sha Alwashin Sassauta Tsadar Abinci, Rayuwa


Shugaba bola Tinubu (Hoto: Facebook/Bayo Onanuga)
Shugaba bola Tinubu (Hoto: Facebook/Bayo Onanuga)

A cewar shugaban kasar, gwamnatinsa na samun nasara a yakin da take yi da ta'addanci da 'yan bindiga " da nufin kawar da barazanar Boko Haram da 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa da tsattsauran ra'ayi.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana cewar gwamnatinsa ta maida hankali wajen dawo da zaman lafiya a sassan arewacin kasar dake fama da rikici domin baiwa manoman da 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane suka tarwatsa damar komawa gonakinsu tare da bunkasa noman abinci.

"Muna sa ran ganin bunkasar noman abinci da samun saukin tsadar. Ina daukar muku alkawarin cewa ba zamu gaza akan hakan ba," a cewar Tinubu a yau Talata a jawabinsa na bikin ranar samun 'yancin kan Najeriya na bana a karo na 64, wanda ake gudanarwa a duk ranar 1 ga watan Oktoba.

A cewar shugaban kasar, gwamnatinsa na samun nasara a yakin da take yi da ta'addanci da 'yan bindiga " da nufin kawar da barazanar Boko Haram da 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa da tsattsauran ra'ayi.

Tinubu ya cika bakin cewar gwamnatinsa ta kawar da 'yan ta'adda da kwamandojin 'yan bindiga cikin hanzari fiye da kowace gwamnati.

A cikin shekara guda, gwamnatinmu ta kawar da Boko Haram da kwamandojin 'yan bindiga cikin hanzari fiye da yadda aka taba gani. A bisa kididdigar baya-bayan nan, zaratan dakarunmu sun hallaka fiye da kwamandojin 'yan bindiga da Boko Haram 300 a yankunan arewa maso gabas da maso yamma dama sauran sassan kasar nan," a cewar Tinubu.

Ya kuma bayyana fatan cewar kawar da 'yan bindiga da kwamandojin 'yan ta'adda zai mayar da manoma gonakinsu tare da bunkasa noman abinci.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG