Babban hafsan sojojin kasa na Najeriya, Leftana-janar Tukur Yusuf Buratai, tare da wasu manyan hafsoshi da kwamandojinsa, sun kai ziyara ga sojojin da suke bakin daga a cikin dajin Sambisa a wani matakin ganewa idaonsa irin kokarin da suke yi tare da karfafa musu guiwa.
A lokacin da yake tarbar Janar Buratai da tawagarsa a Bitta, kwamandan Birged ta 26, Birgediya Janar I.M. Obot, yayi bayanin irin nasarorin da suka samu a kan 'yan ta'addar Boko Haram cikin tsakiyar dajin na Sambisa, ciki har da sansanonin da suka kwato da yawa.
Janar Buratai ya yabawa kwamandan da sojojinsa a saboda kwazonsu da sadaukar da kai wajen yakar Boko Haram. Yace shugaba Muhammadu Buhari da kansa ya nuna farin ciki da irin wannan kwazo na kakkabe 'yan Boko haram daga wuraren da suke buya cikin dajin.
Sanarwar da kakakin rundunar sojojin kasa ta Najeriya, Birgediya Janar Sani kukasheka Usman, ya bayar ta ce Janar Buratai yayi ma sojojin alkawarin cewa nan ba da jimawa ba, zasu ga karin kayan fada, kamar motocin MRAP wadanda ke iya jure nakiya da aka binne a kasa tare da kare sojoji daga kwanton bauna.
A nan Bitta, Janar Buratai ya kuma yi jawabi ga sojojin kasar Kamaru dake cikin rundunar yaki da Boko Haram, inda ya gode musu a saboda kwazonsu tare da rokonsu da su ci gaba da yin aiki da takwaroprinsu na Najeriya wajen cimma gurin kawsar da 'yan Boko Haram baki daya daga duk inda suka buya.
Haka kuma, babban hafsan hafsoshin sojojin kasar ya ziyarci wasu wurare cikin dajin na Sambisa kamar Tokombere, inda ya roki sojoji da su ci gaba da matsin lamba a kan 'yan Boko Haram dake kokarin tserewa.
A Sabil Huda, an zagaya da Janar Buratai ya ga sansanonin wasu bataliyoyin yaki, da rijiyoyin burtsatse da aka tona na samar da ruwa da kuma wasu daga cikin motocin yakin da aka kwato daga hannun 'yan Boko Haram.
Facebook Forum