A karshen makon da ya gabata, aka yi jana’izar daliban firamare 20, wadanda gobara ta hallaka a Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar.
Iyalai da ‘yan uwan wadannan dalibai tare da jami’an gwamnati, sun halarci jana’izar daliban, wadanda aka lullube akwatunan gawarsu da tutar kasar, aka kuma binne su a makeken kabari daya a birnin na Yamai.
Wata wuta da iska ta rura ce ta mamaye makarantar firamaren, wacce ke wajen birnin kasar, ta kuma hallaka yara 20 wadanda shekarunsu ke tsakanin 7 zuwa 13 yayin da suke ajujuwansu a ranar Talata.
Hukumomi sun ce, gobarar ta yadu cikin sauri, yayin da kusan dalibai 2,000 ke daukan karatu.
Karin bayani akan: dalibai, daliban, Yamai, da Jamhuriyar Nijar.
“Za mu yi iya bakin kokarinmu domin ganin hakan bai sake faruwa ba,” in ji Ministan cikin gida Alkache Alhada, wanda ya yi magana bayan halartar janai’zar.
Ya zuwa yanzu ana kan binciken musabbabin wannan gobara wacce ba a san daga inda ta taso ba.
Ko da yake, a ranar Laraba malamai da iyaye, sun ce wannan bala’i da ya auku, na nuni da irin hadarin da ke tattare da ajiye dalibai yara a ajujuwan wucin gadi. A lokuta da dama, akan yi Amfani da ciyawa ne wajen kafawa dalibai ajujuwa a makarantun da ke da yawan cunkoso.
Labarai masu alaka
Zangon shirye-shirye
-
Disamba 31, 2024
Waiwaye Kan Labarai Da Suka Daukar Hankali A 2024
-
Disamba 20, 2024
Ana Ci Gaba Da Fama Da Karancin Takardan Naira A Najeriya
-
Disamba 20, 2024
Hira Da Audu Bulama Bukarti A Birnin Landan Na Kasar Birtaniya
-
Disamba 07, 2024
Yadda Aka Kirga A WaninRumfar Zabe A Greater Accra
-
Disamba 07, 2024
An Fara Kirga Kuri'un Zaben Ghana