Jamus, kasar da ta fi samun kwanciyar hankali a kungiyar tarayyar Turai, ta sami kanta cikin rikicin siyasa yau litinin.
Makonnin da aka kwashe ana shawarwari a kan kafa gwamnatin hadin guiwa a kasar ya rushe, yayinda jam'iyun kasar hudu dake ganawar suka kasa jituwa akan batun bakin haure, da manufofin makamashi, da kuma kara hadin kan tarayyar Turai.
Ana sa ran shugabar gwamnati, Angela Merkel, zata gana da shugaban kasar, amma har yanzu babu tabbacin ko zata kafa gwamnatin tsiraru, wanda hakan zai hana a yi zaben ‘yan majalisa na ba a kan wa'adi ba, ko kuma ta bada shawarar a yi zabe a farkon shekara mai zuwa.
Rahoton kasa cimma wani abin kirki a ganawar ya janyo faduwar darajar kudin Euro a kasuwanin hada-hadar kudade a Asiya inda takardar kudin ta yi kasa idan an kwatanta da dalar Amurka da kudin Japan.
Kalubalen da shugaba Merkel take fuskanta suna zuwa ne a wani muhimmin lokaci ga kungiyar tarayyar turai, wadda ke fuskantar shawarwari maras dadi kan ficewar Britaniya daga cikin kungiyar.
Facebook Forum