Jam’iyyar adawa ta PDP ta jinjinawa shugaban Najeiya Muhammad Buhari da ya yi saurin kai ziyarar jaje zuwa jihar Plato biyo bayan kashe mutane 86 sanadiyar rikicin manoma da makiyaya.
Jami’in yada labaru shugaban jam’iyyar Shehu Yusuf Kura, yace haka ya dace shugaban Najeriya ya dinga yi. Shehu Kura y ace maimakon zuwa bude ayyuka a jihar Cross Rivers ta PDP da shugaban ya yi kamata ya yi a ci gaba da duba kalubalen tsaro a Zamfara, Birnin Gwari da dai sauransu.
Shehu Kura y ace amma dai ba’a makara ba kuma suna fatan zuwansa zai sa a lalubo bakin zaren rigingimun. Ya ce ya je jaje jihar Bauchi da jihar Plato kuma suna fatan duk inda aka samu tashin hankali shugaban kasa zai daure ya je.
Yayinda ake kashe mutane kullum a kasar Shehu Kura a madadin PDP na cewa ya makata gwamnati ta zauna ta shawo kan matsalolin idan da gaske take da samar da tsaro a duk fadin kasar.
A saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani
Facebook Forum