Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya baiwa al’ummar jihar Plato shawarar su hada kai domin tabbatar da zaman lafiya tsakaninsu.
Shugaban ya bada shawarar ce yayinda ya kai ziyarar jaje a Jos babban Birnin jihar, biyo bayan wani mummunan rikicin da ya yi sanadiyar asarar rayuka 86 da dimbin dukiyoyi.
Ya gana da masu ruwa da tsaki a jihar inda ya yi tur da tashin hankalin kana ya shawarci shugabannin al’ummomi daban daban da su koma yankunansu su rarrashi jama'a su rungumi zaman lafiya.
Ya bukaci su mika ta’aziyarsa ga ‘yanuwan wadanda suka rasa rayukansu da dukiyoyinsu. Ya kuma yi kira gare su da su kasance shugabannai ga al’ummarsu, su lalashesu su yi hakuri da juna.
Gwamnan jihar Plato Simon Lalong ya yabawa gwamnatin tarayya kan matakan da ta dauka domin dakile rikicin. Matakan sun hada da samar da jiragen sama na bankado bata gari da kuma tura karin jami’an tsaro da kayayyakin aiki a yankunan da ake samun tashin hankali.
Gwamnan yace ba’a saba ganin irin makaman da aka kai hari dasu ba a jihar. Y ace wannan ya nuna ayyukan ta’addanci ne saboda haka ya kamata a dauki irin matakan da aka dauka wajen yaki da ‘yan Boko Haram. Ya roki shugaban kasa da ya baiwa jami’an tsaro umarnin, su bi gida gida su tattara makaman dake hannu mutane. Yin hakan, zai fito da dimbin makaman dake jihar. Ya kuma ja kunnuwan masu ruwa da tsaki su daina yin katsalandan a duk lokacin da aka kama masu laifi domin a hukunta su.
Dambo Jibo wani shugaban jama’a a yankin yace sun yi maraba da matakin kafa sansanin ‘yan sanda a Gashish amma abun da ya fi a’ala shi ne ‘yan Najeriya su kuduri aniyyar zaman lafiya da juna. Shi ko Ardo Yakubu Dabo Boro, ardo na Bokkos y ace kafa sansanin na ‘yan sanda a Gashish zai taimaka sosai.
Bulus Bot yace duk wanda aka kai wurin idan baya tsaoron Allah za’a koma gidan jiya.
A saurari rahoton Zainab Babaji da karin bayani
Facebook Forum