Jiya Talata ta kasance ranar farin ciki ga ‘yan Democrat a Amurka bayan da jam’iyar ta lashe zaben gwmanonin da aka yi a wasu jihohi.
Dan takarar Democrat, Ralph Northam ya lashe zaben jihar Virginia, wanda ya kasance zazzafa, inda ya doke abokin hamayyarsa Ed Gillespie, nasarar da ta bashi damar maye gurbin gwamna mai barin gado, Terry McAullife, wanda dan jam’iyar ta Democrat ne.
A jihar New Jersey kuwa, dan takarar jam’iyar ta Democrat, Phil Murphy ya samu galaba akan abokiyar hamayyarsa Kim Guadagno, ‘yar Republican, inda zai maye gurbin gwamna mai barin gado, Chris Christie na jam'iyyar Republican.
Dama dai ana sa ran dan takarar na Democrat shi zai lashe wannan zabe.
Har ila yau a zaben na Virginia, dan takarar Democrat Danica Roem ya samu nasara akan Robert Marshall, nasarar da ta bashi damar zama dan majalisar dokokin jihar na farko da ya fito fili ya bayyana cewa ya sauya jinsinsa.
Wannan zabe da aka yi a jiya Talata, zai iya zama mahangar yadda masu kada kuri’a suke kallon kamun ludayin gwamnatin shugaba Trump, yayin da jam’iyun biyu ke ta da tsiminsu domin tunkarar zaben rabin wa’adi da za a yi a badi a duk fadin Amurka.
Facebook Forum