Cikin jawabin da yayi gwamna Sule Lamido ya zargi gwamnonin PDP, musamman Gwamna Wamako da suka fice daga PDP a matsayin wadanda suka yiwa jam'iyyar buturci.
A cewar Gwamna Lamido jam'iyyar PDP ita ce ta kai gwamnonin matasyin da suke yanzu. Yace idan jam'iyyar PDP yanzu ta zama ta masu kama karya to ai an kama an karya kana an ba Gwamna Wamako ya zama gwamnan Sokoto. Kenan da kama karya ya zauna akan mulkinsa.
Kalaman na Gwamna Sule Lamido basu yiwa jam'iyyar APC dadi ba. Dalilinsu ke nan na kiran taron 'yan jarida domin su mayarda martani. Dr Abubakar Muhammad Sokoto daya daga cikin dattawan jam'iyyar yace maganganun na Gwamna Sule Lamido bai makata ya yisu ba. Shi ne ma yakamata ya zama mutum na karshe da zai yi irin wadannan furucin. Tafiyar ficewa daga PDP dashi aka farata. Daga baya ya shiga wani rikici yayin da aka samu dansa da rashin gaskiya.
Dole Gwamna Lamido ya koma cikin marasa gaskiya domin su ne masu kare marasa gaskiya. Sabii da haka ba daga gareshi yakamata a ji cewa wasu sun yi butulci domin shi kansa an ganshi cikin kazanta. Shi kansa domin a kare mashi rashin gaskiya ya sa ya dake a PDP. Irinsu Lamido suna cikin rashin gaskiya dumu-dumu domin haka basa iya fita daga PDP domin kada a yi masu bita da kuli.
Wamako ya daure. Shi dai idan ana son a yi wani abu wa jama'arsa to a dawo a yi gaskiya.
To saidai Gwamna Lamido ya bayyana dalilinsa na kin barin PDP. Duk da neman bata masa suna shi Sule ba zai bar hakin shugabanci ba a yi masa hauka. Shugaba ya kan yi hakuri a wulakantashi. Shugaba hakuri ya keyi ya kuma karbi kaddarar abun da Allah ya aiko.
SAUTI: Jam'iyyar APC Ta Mayarwa Gwamna Lamido Martani - 2' 56" http://bit.ly1ukeYOJ
HOTO: Tambarin APC
#Hausa #Nigeria
Ga rahoton Murta Faruk Sanyinna.