To saidai wasu suna harsashen irin wadannan kalamun suna da hadarin gaske.
Tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara ta fuskar siyasa Barrister Ahmad Gulak yace a cigaba da addu'a Allah ya yiwa kasar jagora da bada zaman lafiya.
Dan takaran gwamnan jam'iyyar PDM a Taraba Kabiru Dodo na ganin cewa Najeriya ta sha tsallake siradin guguwar fitina. Yace furucin 'yan siyasan al'ada ce ta dan Adam. Yana jin tsoron abun da bai shirya masa ba yana kuma tsoron abun da ya shiryawa. A shekarar 2003 an ce idan an yi zabe kasar zata ruguje amma hakan bai faru ba. Haka ma aka fada a 2007 da 2011 amma kasar ta cigaba.
Yace idan da ba'a hana kasar samun shugabanci nagari ba babu kasar dake da dadin zama irin Najeriya. Allah ya albarkaci kasar da masu ilimi da masu sanin yakamata. Idan da kashi goma na abubuwan dake faruwa a kasar sun faru a wasu kasashen to da tuni an manta dasu.
Wasu daga jihohin da aka tsaurara matakan tsaro na ganin furta kalamun kushe ga shugabanni na hana cin moriyar dimokradiya.Suna cewa kamata yayi mutane su zama masu hakuri da juna. Idan gwamnati tayi abun kirki a yaba mata a kuma daina abubuwan da basu da alheri a ciki. Idan kullum ana yiwa shugabanni addu'a jama'a zasu ga da kyau. Idan kuma ana kushewa abun alheri to alherin ba zai zo ba.
Daga bisani wani yace idan aka tabbatar da gaskiya a zabe babu wanda zai tada fitina. Abu ne mai muni idan aka karkata sakamakon zabe a ka baiwa wadanda basu ci ba.
Ga rahoton Saleh Ashaka.