Rogers mawaki ne kuma darakta , wasu lokutan ma ya kan yi wakar fina-finai, ko da yake, a yanzu ya fi maida hankali wajen rera wakoki.
Ya ce a yanzu ya dakatar da bada umarni domin yana da daukar lokaci, sannan baya bada kudi yadda ya kamata kamar yarda wakar ta fi kawo wa, ya kuma kara da cewa waka ta fi saurin bada tasiri a cikin al’umma.
Jamilu Roger ya ce ko da yake a yanzu ya fi maida hankali a wakokin addini, yana ba da gudunmuwa yadda ya kamata na zaman lafiya da kuma yada addinin sa.
Roger ya kara da cewa, ko da yake ya fara ne da Kannywood inda yake rike kamara, daga baya ya fito jarumi har ta kai shi ga wakokin fina-finai, sannan yanzu kuma ya tsunduma ga waka zalla.
Ya ce harkar wakoki ta fi sauki fiye da harka ta fim, domin a kullum ana samun canji na rayuwa sannan ko a wajen biyan hakki ba ya daidai da na waka, kuma ga ba da saurin isar da sako da waka ke yi.
Daga cikin kalubalen da yake fuskanta a mawaki, shi ne idan ya tashi da niyyar waka bayan ya je studio sai ya tarar da cunkoson jama’a, kafin a zo kansa sai karsashin da ya zo da ita ta gushe.
Wannan na daga cikin manyan kalubalen da mawaka ke fama da shi.
A saurari cikakken hirarsu da wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir.
Facebook Forum