Kwamandan ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da suka yi a birnin Maiduguri da wasu Fulani makiyaya kan irin matsalolin dake addabarsu.
Baicin gano wasu daga cikin shanunsu, kwamandan ya shaida cewa taron da Fulanin domin a lalubo hanyoyin da za'a bi a dakile yadda ake sace dukiyar makiyayan ne tare da kashesu da sau tari 'yan Boko Haram suke yi masu musaamman a daji yayindda suke kiwo.
Kwamandan yace a shirye suke su taimakawa makiyaya, su karesu da kuma dukiyarsu musamman a wannan lokacin na karshen shekara lokacin da laifuka ke karuwa. Ibrahim Abdullahi yace sun fahimci cewa makiyaya a jihar Borno sun shiga halin kakanikayi ganin yadda ake sace shanunsu tare da kashe wasunsu a daji.
Ibrahim ya kira makiyayan da su kawo rahoton duk abun da basu yadda dashi ba su kuma zasu dauki matakan da suka dace.
Inji kwamandan 'yan Boko Haram idan sun saci shanu sai su ba wasu dake hada baki dasu su sayar a kasuwanni su karbi kudin domin sayen magani da makamai. Gwmnan jihar da ya damu da alamarin ya shigo da jami'an tsaron farin kaya tunda ba za'a hada baki dasu ba a cuci jama'a ko a basu cin hanci.
Mutane ukun da suka kama daya yace shi direban Boko Haram ne, daya kuma yace shi dan kungiyar ne shi kuma na ukun shi ne dan aike mai shafe masu fagge idan zasu aikata wani abu.
'Yan kungiyar Miyetti Allah ta Fulani sun bayyana farin cikinsu da abun da ya faru. Sun ce ana zuwa a kwashe dukiyoyinsu kakaf a kuma kashe wasu cikinsu.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.