Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an 'Yan Sandan Kasar Brazil Ka Iya Tuhumar 'Yan Wsan Ninkayar Amurka


Jami’an ‘yan sandan kasar Brazil sun ce mai yiwuwa su tuhumi ‘yan wasan ninkayar Amurka da laifin barnata duniyar jama’a da kuma bayar da bayanan ‘karya, bayan da ‘yan wasan su ka amsa cewa sun kirkiri labarin ‘karya da suka ce anyi musu fashi da makami.

‘Yan wasan Ninkayar Ryan Lochte da Jack Conger da Gunnar Bentz da kuma James Feigen, da farko dai sun fadawa ‘yan sanda cewa anyi musu fashi da bindiga a safiyar ranar Lahadi, kan hanyar su ta komawa masaukinsu.

Amma ‘yan wasan biyu Conger da Bentz, sun fito sun fadi gaskiya cewa kirkirar labarin kawai su kayi, bayan da aka tsare su a filin saukar jigaren sama da yammacin ranar Laraba, lokacin da

suke kokarin komawa kasarsu wato Amurka. Shima Feigen yanzu haka yana Brazil, yayin da Lochte ya dawo Amurka tun ranar Litinin kafin ma labarin ya fito.

A jiya Alhamis shugaban ‘yan sanda a Rio, Fernando Veloso, ya fadawa manema labarai cewa hotunan bidiyo sun nuna cewa ‘yan wasan sun ziyarci wani gidan Mai ne a safiyar Lahadi, kuma wani shaida yace sun lalata bandaki, inda wani maigadi yayi musu magana, suka kuma bar gurin kafin ‘yan sanda su karaso.

A jiya Alhamis din ne gidan Talabijin na Glovo TV ya haska hotan bidiyon dake nuna isar ‘yan wasan zuwa gidan Man cikin motar taxi, da lokacin da suke shiga cikin ginin da kuma lokacin da suke barin gidan Man, can kuma sai gasu sun zauna da hannayensu a sama kamar yadda ‘daya daga cikin ma’aikatan gidan Man ya umarcesu.

XS
SM
MD
LG