Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami’an Tsaro Na Tabbatar Dokar Hana Zirga-Zirga A Birnin Kano


Masu murnar lashe zabe a birnin Kano
Masu murnar lashe zabe a birnin Kano

Rundunar ‘yan sada ta jihar Kano ta ce jami’anta na sanya ido sosai domin tabbatar da cewa, al’umar jihar sunyi biyayya sosai ga dokar hana zirga zirgar Jama’a a birnin da kewayen Kano, wadda ta fara aiki tun da sanyin safiyar ranar Litinin.

Gwamnatin jihar Kano ce ta sanya dokar a wani mataki na kare rayuka da dikiyar Jama’a.

Tun a ranar Lahadi yanayin tsaro a sassan jihar Kano ya shiga damuwa, bayan da hukumar zaben Najeriya ta fara tattara sakamakon zaben gwamna da ya wakana a ranar Asabar, al’amarin da ya sanya hukumomin tsaro suka tsaurara matakan tsaro.

Al’amura sun kara zafafa daga daren Lahadi zuwa wayewar garin Litinin, musamman gabanin hukumar INEC ta sanar da mutumin da ya yi nasara a zaben.

Comrade Mohammed Garba, shine kwamishinan labaru na Kano, ya ce la’akari da nauyin dake rataye wuyan gwamnati na tabbatar da aminci a tsakanin al’uma tilas ta dauki wannan mataki.

Ya ce tuni gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bada umarni lallai a sanya hana zirga zirgar Jama’a, haka kuma gwamnati bisa hadin gwiwa da hukumomin tsaro na aiki tare domin ganin cewa, dokar ta yi aiki yadda ya kamata.

Masu murnar lashe zabe a birnin Kano
Masu murnar lashe zabe a birnin Kano

Sai dai ga alama matasa, musamman magoya bayan Jam’iyyar da ta yi nasara sunyi dandazo a titunan birnin Kano suna harkokin nuna murnar cin zabe.

Amma kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano Hussaini Muhammad, ya gargadi matasan da cewa su gudanar da harkokin su na murna cikin yanayi na kiyaye doka da oda. Yana mai cewa, Jami’an tsaro ba za su nade hannun su ba yayin da wasu ke yunkurin amfani da yanayin nuna murna su lalata dukiyar Jama’a.

Sai dai duk da haka, begen murnar dai ya sanya matasan lalata abubuwan amfani a galibin sassan birnin Kano, musamman allunan tallar hajar kamfanoni da alluna masu dauke da hotunan ‘yan siyasa da sauran ababe, duk kuwa cewa, an girke Jami’an tsaro a wurare daban daban na birnin Kano baya ga shawagin da jirgi mai saukar ungulu ke yi a sararin samaniyar birnin.

Domin Karin bayani saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG