Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin kasar ta soma zaman makokin kwanaki 3 daga yau juma’a a, da nufin nuna alhinin rasuwar sojojinta sama da 70 sakamakon harin ta’addanci da aka kai a barikin Inates,
A sanarwar hadin gwiwar da suka fitar a yammacin jiya Alhamis ‘yan adawa da masu rinjaye a majalisar dokokin sun fara ne da jajantawa ‘yan kasa a game da wannan babban rashi.
‘Yan majalisar sun kuma jinjinawa dakarun da suka kwanta dama a yayinda suke kokarin kare martabar Nijer da jama’arta.
La’akari da hanyoyin da ‘yan ta’adda ke amfani da su a hare haren da suka kai a ‘yan makwanin nan a kasashen Mali Burkina Faso da jamhuriyar Nijer ya sa majalisar jan hankulan kasashen duniya su farka daga barci..
Gwamnatin jamhuriyar Nijer a cewar kakakinta Zakaria Abdourahamane, ta ware kwanaki 3 na zaman makoki daga yau juma’a da nufin nuna alhinin wannan rashi sannan ta bukaci kowane dan kasa ya ware minitoci 5 daga karfe 10 na safiyar yau domin yin addu’oi ga sojojin da suka rasu akan aikin tabbatar da tsaron kasa..
Da hantsin wannan juma’a ne za a yi jana’izar sojoji 71 din nan da suka kwanta dama a yayin gumurzun da suka yi da ‘yan ta’adda da suka kai hari a barikin sojan Inates kan iyakar Nijer da Mali a ranar talatar da ta gabata.
Kasashen duniya na ci gaba da aikewa da sakwannin ta’aziya ga kasar ta Nijar.
Jakadan Amurka a Nijer Eric P. Whitaker ya bayyana cewa kasarsa ta yi matukar kaduwa da faruwar wannan al’amari sai dai Amurka ba zata taba gajiya ba wajen tallafawa Nijer a yakin da ta kaddamar da yaki da ta’addanci.
Ga karin bayani daga Souley Moumouni Barma
Facebook Forum