Wani alkali a Jihar Colorado a yankin yammacin Amurka ya bayarda umurnin a ci gaba da tsare mutumin da ake tuhuma da bude wuta kan jama’a na wani gidan sinima, James Holmes, a kurkuku, har zuwa lokacin da zai sake bayyana a gaban kotu inda watakila za a gabatar da tuhume-tuhumen da ake yi masa.
Masu gabatar da kara sun fada jiya litinin cewa zasu bukaci da a yanke ma Holmes hukumcin kisa idan an same shi da laifi. Ana zarginsa da laifin kashe mutane 12 tare da raunata wasu 58 da tsakar daren Jumma’a, lokacin da ake nuna sabon Fim na Batman mai suna “The Dark Night Rises.”
Holmes, wanda ya rina gashin kansa zuwa launin bawon lemo, bai ce uffan ba, haka kuma an ga alamun gigita a jikinsa lokacin da ya bayyana jiya litinin a gaban kotun. Alkalin ya fada masa cewar yana iya fuskantar tuhumar kisan kai.
Hukumomi su na binciken James Holmes da kuma yadda aka yi wannan dalibi mai karanta digirin digirgir ko PhD a fannin Kimiyyar hanyoyin sarrafa sakonni na jikin bil Adama, ya rikide ya koma mutumin da ake zargi da kisan kai.
‘Yan sanda suka ce Holmes ya ki yin magana.