Magoya bayan shugaba Donald Trump na Amurka, suna shirin maida martani ta yanar gizo kan littafin tarihin rayuwar James Comey, da tsohon darektan hukumar ta FBI ya rubuta.
Kwamitin gudanarwa na jam'iyyar Republican, jiya Alhamis, ya kaddamar da wani shafi a internet da suka lakabawa suna LyinComey.com, wadda a ciki suka wallafa kalaman fitattun 'yan jam'iyyar Democrat suna sukar tsohon darektar na FBI a lokutan baya.Jam'iyyar ta Republican tana da niyyar bibiyar sahihancin littafin, kuma tayi amfani da shafin wajen nuna kare-rayi da sabani dake cikin littafin, kamar yadda tashar talabijin ta Fox ta bada labari.
Littafin na Comey mai suna "A Higher Loyalty: Truth, Lies and Leadership, da turanci, ranar Talata mai zuwa ake sa ran fara sayar dashi ga al'umma.
Kamfanin dillancin Labarai na Associated Press yace, Comey ya caccaki Trump, a zaman mutumin da bashi da da'a, wanda ba ruwansa da fadin gaskiya. Ya kwatanta shugabancin Trump,mai dogaro ko gudana kan tinkaho da jiji-da-kai da kuma biyayya sau da kafa kan gaskiya da kariya.
Facebook Forum