Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jama’ar Arewacin Najeriya Na Murnar Mutuwar Kasurgumin Shugaban 'Yan Bindigan Nan Dogo Gide


Dogo Gide - Shugaban ‘yan bindiga a arewacin Najeriya
Dogo Gide - Shugaban ‘yan bindiga a arewacin Najeriya

Masana tsaro da sauran jama'a a Najeriya na ci gaba da tsokaci tare da nuna jin dadi, a kan labarin mutuwar kasurgumin ‘dan bindigan nan Dogo Gide da aka tabbatar da mutuwar sa a jihar Sokoto.

SOKOTO, NIGERIA - An wayi safiyar yau Laraba da samun bayanai na zagayawa a shafukan yanar gizo masu nuna cewa kasurgumin ‘dan ta'addan nan Dogo Gide ya kwanta dama a wani asibiti a Sokoto.

Akan hakan ne Muryar Amurka ta yi tattaki domin gudanar da bincike akan wannan lamarin, kuma bayanai da muka samu daga wani jami’in tsaro wanda baya da iznin magana a hukumance ya shaida mana lallai Dogo Gide ya kwanta dama.

Bayanin ya nuna cewa Dogo Gide ya samu raunuka ne na harbi sanadiyar arangama da jami'an soji na shirin samar da tsaro na hadarin daji, amma sai wani babban jami'in tsaro tare da taimakawar wasu kananan jami'an suka yi masa hanya kuma suka kai shi wani asbiti dake Sakkwato a Unguwar Mabera duk da yake ba a bayyana mana sunan asibitin ba.

Kuma ya ce tuni an tura jami'ai sun kama babban jami'in tsaron da ake tuhuma da hannu ga kawo Dogo Gide a Sokoto.

Da Muryar Amurka ta binciki batun yaya gawar ta Dogo Gide take yanzu ko tana hannu ko asibiti, ya ce zai yi mana karin bayani daga baya.

Yanzu dai jama'a na ci gaba da tofa albarkacin bakin su a kan wannan batun na mutuwar Dogo Gide, wanda jama'a da yawa suka koka da shi akan yadda ya addabe su a baya.

Saurari cikakken rahoto daga Muhammadu Nasir:

Jama’ar Arewacin Najeriya Suna Muryar Mutuwar Gide Shugaban ‘Yan Ta’adda .mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG