Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam’iyyar NDC A Ghana Ta Sauya Shugabanninta A Majalisar Dokokin Kasar


Majalisar dokokin Ghana
Majalisar dokokin Ghana

Jam’iyyar NDC ta canza shugaban marasa rinjaye da mataimakinsa da kuma bulaliyar majalisa, inda ta maye su da wasu. Hakan ya bayyana ne a wata wasika mai dauke da sa hannun babban sakatare Fiifi Kwetey, zuwa ga Alban Bagbin kakakin majalisar dokokin kasar.

A cewar jam’iyyar, dan majalisa mai wakiltar mazabar Ajumako Enyam Essiam Dokta Cassiel Ato Forson ne zai maye gurbin Haruna Iddrisu a matsayin sabon shugaban marasa rinjaye. Shi kuma dan majalisa mai wakiltar mazabar Ellembelle, Kofi Armah Boah zai maye gurbin James Klutse Avedzi a matsayin mataimakin shugaban marasa rinjaye. Sai Kwame Agbodza zai maye gurbin Muntaka Mubarak a matsayin bulaliyar majalisa.

'Yan Majalisar Ghana
'Yan Majalisar Ghana

Tuni dai wasu ‘yan majalisar daga jam’iyyar NDC da dama, da suka hada da dan majalisa mai wakiltar Bolgatanga ta Gabas Dominic Ayine da kuma dan majalisar Tamale ta tsakiya Murtala Muhammed suka bayyana cewa sauye-sauyen basu dace da tsarin damokradiyya ba, domin ba a tuntubi mambobin marasa rinjayen majalisar ba.

Da yake kare matakin, shugaban jam’iyya Johnson Asiedu Nketia, ya ce sakon yakin neman zaben 2024 na jam’iyya zai mayar da hankali ne kan tattalin arzikin kasa, a saboda haka ne aka yanke shawarar sauya shugabanninta a majalisar.

“Yakin zaben 2024 zai kasance ne kan tattalin arziki. Don haka idan jam’iyyarku tana da niyyar yakin lashe zabe, tilas ne ku ajiye kafafunku kasa don samun nasara a muhawarar.”

A saboda haka ne suka sauya lauya Haruna Iddrisu a matsayin shugaban marasa rinjaye zuwa masanin tattalin arziki Dokta Cassiel Atto Forson. Wannan dalilin bai samu karbuwa ba a wurin mabiya jam’iyya, musamman a mazabar tsohon shugaban majalisar da ke birnin Tamale.

Al’ummar Dagbon, da al’ummar Musulmai, da ta yankin Arewa ba su fahimci abinda ke faruwa ba, a cewar wasu mabiya jam’iyyar. Sun kuma bukaci shugaban jam’iyya da babban sakatare Fiifi Kwetey su janye hukuncin da suka yanke, idan ba haka ba bayan sa’o’i 24 za su ga abinda zai faru.”

Sai dai jami’an sadarwar jam’iyyar sun yi kira ga magoya baya da su yi hakuri an dauki matakin ne don samun nasarar jam’iyya a zabe mai zuwa kuma hakan na nuni da cewa suna kwatanta dimokradiyya.

Rahotanni na nuna cewa, ‘yan majalisa arba’in da takwas na jam’iyyar NDC sun rattaba hannu kan wata takardar korafi ga shugabannin jam’iyyar, a kan su janye wannan hukunci na sauya shugabannin jam’iyyar a majalisar dokoki.

Saurari cikakken rahoton Idris Abdallah Bako:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

XS
SM
MD
LG