Wannan muhawarar ta taso ne saboda wani muhimmin tanadi da yake cikin dokar da ke cewa, katin shaidan dan kasa (Ghana Card) kadai ne zai baiwa ‘yan kasar damar cancantar mallakar katin zabe.
Mataimakin shugabar hukumar zabe ta Ghana, Mista Sammuel Tettey, fada a taron manema labarai da hukumar ta shirya a birnin Accra cewa, “Mun tattauna a kai da IPAC (Kwamitin shawarwari tsakanin jam'iyyu) kuma mun aika da shi ga AG (Antoni Janar na kasa). A zahiri ana tattaunawa kuma ba mu gabatar da shi a majalisa ba tukuna; domin majalisa a halin yanzu tana hutu za mu gabatar idan sun dawo daga hutu.”
Mista Tettey ya ce tsarin yin garanti ga wanda ba shi da cikakken takardun shaidar dan kasa, yana cike da kalubale da dama, kuma ba zai iya samar da ingantaccen tsarin rajistar masu zabe ga kasar ba, domin haka za a soke hakan.
Dangane da rajistar masu kada kuri’a kuwa, hukumar ta ce ba za ta hada sabuwar rajistar masu zabe na dan lokaci kamar yadda aka saba ba, amma za a dinga yin rajistar ne a ko da yaushe da zarar dan kasa ya cancanci mallakar katin. Domin haka hukumar na tsammanin yin rijistar mutane tsakanin 450,000 zuwa 550,000 a kowace shekara.
Wadannan sauye-sauyen da hukumar ta yi, ya dace da ra’ayin jam’iyar NPP mai ci. Jami’in sadarwar jam’iyyar kuma mamba a majalisar gundumar Ga ta Yamma, Issaka Ibrahim, ya ce tun da yake kowa ya amince cewa, katin zama dan kasa shi ne shaidar da ta fi cancanta, to kafin a yi zabe kowa zai iya samu kuma ya yi amfani da shi wajen samun katin zabe, da yake hukumar ta ce a ko da yaushe ‘yan kasa za su iya zuwa a yi musu katin.
Sai dai babbar jam’iyar adawa ta NDC da sauran jam’iyyun adawa ba su amince da kudurin hukumar zaben ba, domin yin hakan zai tauyewa jama’a da dama ‘yancin sun a kada kuri’a.
Babban jami’in sadarwan Zango na kasa na jam’iyar NDC, Mohammed Nazeer, ya ce idan an kai ga majalisa za su nunawa ‘yan Ghana cewa wannan kudurin da hukumar zabe ta dauko ba dimokaradiyya ba ne.
Shi kuma Seeba Shakibu, babban sakataren jam’iyar PNC, reshen yankin Accra ya ce lallai idan an tabbatar da wannan kudurin zai tauye hakkin masu jefa kuri’a kuma jam’iyyar sa ba ta amince da hakan ba.
A karshe hukumar zabe ta yi kira ga Hukumar Shaidar ‘yan kasa (NIA) da ta gaggauta bugawa tare da rarraba katunan shaidar ‘yan kasa domin baiwa wadanda suka cancanta samun saukin yin rijistar katin zabe.
Saurari cikakken rahoton Idris Abdalla Bako: