Jakadun kasashen Afrika da dama sun rubuta wa ma'aikatar harkokin wajen China wasika a makon da ya gabata suna kira kan su sa baki a daina yin amfani da karfi wajen yin gwaji, killacewa da kuma cin zarafin ‘yan Afirka.
A ranar Asabar 11 ga watan Afirilu ne ma’aikatar harkokin wajen Ghana ta bukaci jakadan China ya mika korafin gwamnatin Ghana ga hukumomin China.
Sai dai ma’aikatar harkokin wajen China ta fada a ranar Litinin 13 ga watan na Afirilu cewa bata nuna wa ‘yan kasashen waje wariya.
Wani matashi dalibi dan shekaru goma sha tara da haihuwa, dan asalin kasar Ivory Coast, wanda ya nemi mafaka a karkashin wata gada dauke da 'yar jakkarsa, ya ce ya yi ta kokarin kiran mutanen da ya sani a China.
Ya bayyana cewa ya je China ne don ya koyi harshen kasar amma kuma an rufe jami’ar da yake karatun saboda annobar cutar coronavirus. Dalibin ya ce Otel da dama da ya nemi masauki sun ki karbara sa, amma ya ce ya samu wani guda daya a ranar Litinin.
Facebook Forum