Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Zata Rage Ofisoshin Jakadancinta


 Shugaba Muhammad Buhari
Shugaba Muhammad Buhari

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya bada tabbacin kasar zata dauki matakan rage ofisoshin jakadancinta dake kasashen duniya

Shugaban ya bayyana haka ne lokacin da jami'an ma'aikatar harkokin waje a karkashin jagorancin Ambassador Bulus Lolo suka kai masa ziyara.

Ambassador Lolo da tawagarsa sun yiwa shugaban kasa bayanin bukatun ma'aikatar da zummar tabbatar da an dauki hakokin ma'aikata da na ofisoshin jakadanci domin su zo daidai da bukatun Najeriya.

Yayinda yake mayarda martani shugaba Buhari yace kowane lokaci daga yanzu za'a kafa wani kwamiti na shugaban kasa domin tabbatar da an dakuki matakai da hanyoyin da za'a bi na rage ofisoshin jakadancin kasar su dace da bukatu da kuma karfin Najeriya.

A kan wannan furuci na shugaban ne ya sa Muryar Amurka ta gana da Ambassador Adamu Saidu Daura tsohon jakadan Najeriya a kasashen Jordan da Pakistan domin jin ko akwai tasirin daukan matakin a daidai wannan lokaci.

Ambassador Daura yace babu shakka akwai hujjar daukan matakin domin yawan ofishin jakadanci kasa ya nuna yawan tattalin arzikinta ne. Kowace kasa takan bude ofishin jakadanci daidai fahimtarta na karfinta. Ta kan kuma duba dangantakarta da kowace kasa bisa ga yawan jama'arta a kasar ko kuma dangantakar kasuwanci mai yawa ne ke akwai da kasar.

Wata kasar kuma zumunci ne mai karfi tsakaninsu musamman kasashen Afirka. Amma tunda yanzu tattalin arzikin kasar ya shiga wani hali yakamata a duba bangaren ofisoshin kasuwanci. Wadanda suke da mahimmanci a karfafasu. Wadanda kuma mahimmancinsu bai kai a dinga zuba kudi kansu ba yayi daidai a rufesu domin talakawa su samu saukin biyan ma'aikata.

Ga rahotn Umar Faruk Musa da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG