Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Israila Da 'Yan Gwagwarmaya Sun Ci Gaba Da Kaiwa Juna Hare-Hare


Wasu na kokarin ceton ran wani wanda harin jiragen saman yakin Israila ya rutsa da shi a Zirin Gaza
Wasu na kokarin ceton ran wani wanda harin jiragen saman yakin Israila ya rutsa da shi a Zirin Gaza

Falasdinawa sun harba rokoki kudancin Israila a yayin da Israila kuma ta kwan dare tana ruwan wuta a Zirin Gaza

Israila da Falasdinawa ‘yan gwagwarmaya masu sansani a Gaza sun ci gaba da kaiwa junan su hare-hare, har ya zuwa yau Lahadi, bayan munanan hare-haren da suka jawo asarar rayuka a jiya Asabar lokacin da Israila ta kai harin jiragen sama kan Falasdinawa ‘yan gwagwarmaya.

Gwamnatin kasar Masar ta yi kokarin shiga tsakani da nufin cimma tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu domin kashe wutar rikicin kafin ya ta’azzara, amma yunkurin na kasar Masar ya ci tura. Da jijjifin Lahadin nan an harba dimbin rokoki a kudancin Israila a yayin da su kuma jiragen saman yakin Israila su ka kwan dare suna ruwan wuta akan sansanonin ‘yan gwagwarmaya a Zirin Gaza.

Falasdinawa ‘yan gwagwarmaya sun fada a yau Lahadi cewa a shirye suke su tsagaita wuta, idan Israila ma ta amince da tsagaita wutar.

Hare-haren da jiragen saman yakin Israila su kai Gaza jiya Asabar kan sansanonin ‘yan gwagwarmayar Islamic Jihad, sun halaka mutum 9. Kungiyar Islamic Jihad ta ce wani kwamandan kungiyar na cikin wadanda hare-haren Israilar suka kashe. Rokokin daukan fansar da Falasdinawa ‘yan gwagwarmaya suka harba cikin Israila sun halaka mutum guda tare da raunata wasu biyu a kalla.

Rundunar sojojin Israila tace hare-haren jiragen saman da ta kai jiya Asabar, ta kai su ne kan wadanda su ka harba rokoki cikin Israila ranar Laraba, duk da cewa babu wanda ya ji ciwo sanadiyar rokokin.

Israila ta bukaci taimakon kasa da kasa wajen dakatar da hare-haren na Falasdinawa. Ministan harakokin wajen Israila Avigdor Lieberman ya fada a jiya Asabar cewa “Israila ba ta neman fada da Falasdinawa kuma ba ta so ta tsananta halin da ake ciki yanzu, amma ba zata yarda ana ta harba ma ta rokoki daya bayan daya ba, ba tare da ta maida martani ba.

MDD ta yi kira a kai zukata nesa. Manzon MDD a yankin GTT Robert Serry, ya ce, yana da muhimmanci tun yanzu a dauki matakin dakile al’amarin tun bai tsananta ba, kuma ba da wani jinkiri ba.

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG