Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Ta Ayyana Yaki Kan Mayakan Hamas


Netanyahu da 'yan majalisar dokokin Isra'ila
Netanyahu da 'yan majalisar dokokin Isra'ila

Firai Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce Isra'ila za ta maida martani mai zafi kan mayakan Hamas da suka kai wa kasarsa hari ranar Asabar.

A hukumance gwamnatin Isra'ila ta ayyana yaki kan mayakan Hamas a zirin Gaza a ranar Lahadi, lamarin da ya share fagen maida martanin soja mai zafi da zata kai sakamakon harin ba-zata da mayaka masu zafin kishin addinin Islama suka kai kan Isra'ila.

Dama tun a ranar Asabar Firai Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya fadi cewa kasarsa ta shiga yaki da Hamas a yayin da mayakan suka kai hare-haren, daga baya kwamitin tsaron majalisar dokokin Isra’ila ya cimma matsayar ayyana yakin a hukumance.

Gabanin kada kuri'ar kwamitin majalisar, Netanyahu ya ayyana cewa Isra'ila za ta "maida martani mai zafi" kan Hamas, ko da yake sojojin Isra'ila sun fafata da mayakan na Hamas a kan titunan kudancin Isra'ila ranar Lahadi, sun kuma kaddamar da hare-haren ramuwar gayya ta sama da suka lalata gine-gine a Gaza.

Firai Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Firai Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu

A fayyace dai ba a san abin da sabon martani mai zafi na Isra'ila zai kunsa ba. Wasu manazarta a yankin Gabas ta Tsakiya sun ce ta yiwu hakan na nufin Isra'ila za ta iya kai wa Gaza hari ta kasa, lamarin da zai ruruta wutar rikicin.

Ko ma wane irin martani ne, Netanyahu ya yi gargadin cewa, “yakin zai dauki lokaci mai tsawo. Za a ji jiki.”

Manjo Janar Ghassan Alian, wani babban jami'in rundunar tsaron Isra'ila, ya ce Hamas ta "janyo bala’i" saboda harin ba-zatan da ta kai, kuma "za ta ga sakamakon abin da ta aikata."

ISRAEL PALESTINA
ISRAEL PALESTINA

Isra'ila ta ce an kashe akalla mutane 600 a kasar, ciki har da sojoji 44, sannan fiye da 1,500 suka jikkata. Jami'ai a Gaza sun ce mutane 313 ne suka mutu a yankin, yayin da wasu kusan 2,000 suka jikkata. Wani jami'in Isra'ila ya ce sojojin kasar sun kashe mayaka 400 tare da kama wasu da dama.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG