Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Gini Ya Rushe A Kasuwar Hannayen Jari A Jakarta


Ginin da ya fadi
Ginin da ya fadi

‘Yan sanda sun ce mutane 75 sun jikkata yau litinin, a lokacin da wata farfajiya ta subuto cikin babban zauren kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Jakarta, inda kankare ya rufe mutane da dama.

Jami’an ayyukan gaggawa sun ce babu rahoton mutuwa da aka samu a lokacin wannan hatsari da ya wakana a ginin kasuwar, inda nan ne Bankin Duniya ma yake da ofishinsa na kasar Indonesiya.

Wata mace mai suna Megha Kapoor dake aiki a cikin ginin, ta ce ta ga fallen kankare yana fadowa, tare da kura. Daga nan sai bututun ruwa ya fashe. Ta ce ta ji karar ballewar wani abu, kuma ta ga wata mace kwance a some, karkashin kankaren da ya fado.

An samu damar komawa ga hada-hadar sayarwa da sayen hannayen jari a kasuwar zuwa tsakar rana.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG