Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ina Tare Da Sadio Mane - Tuchel


Tuchel, dama da Sadio Mane, hagu
Tuchel, dama da Sadio Mane, hagu

Rahotannin sun ce Mane ya naushi Sane a dakin shiryawan ‘yan wasa bayan da kungiyar ta sha kaye a hannun Manchester City a gasar Champions League.

Mai horar da ‘yan wasan Bayern Munich Thomas Tuchel ya ce zai marawa Sadio Mane baya bayan da dan wasan ya ba da hakuri kan sabanin da suka samu da Leroy Sane.

Rahotanni sun ce Mane ya naushi Sane a dakin shiryawan ‘yan wasa bayan da kungiyar ta sha kaye a hannun Manchester City a gasar Champions League.

Hakan ya sa Bayern ta dakatar da shi daga buga wasan da lungiyar za ta yi da Hoffenheim a ranar Asabar.

‘Yan wasan da kungiyar ta Bayern, ba su bayyana asalin abin da ya hada fadan ba.

Tuchel ya ce shi bai ga abin da ya faru ba, amma ya yi magana da Mane da Sane da sauran ‘yan wasan da aka yi abin a idonsu, sun kuma ce Mane ya ba da hakuri kan abin da ya aikata.

“Ni ne zan zama lauyansa na farko wanda zai kare shi. Na san shi (Mane) na tsawon lokaci, na kuma san halinsa. Zai samu cikakken goyon bayana . Kowa zai iya yin kuskure a rayuwa.” Tuchel ya ce.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG