Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Idan Aka Yi 'Sake'Yan Ta'adda Na Iya Samun Mafaka A Ghana - Yan Sanda


Rikicin Bawku.
Rikicin Bawku.

Hukumar yan sandan kasar Ghana ta sanar da daukar matakin karfafa tsaro a iyakokin kasar da Burkina Faso, biyo bayan bankado cewa wasu al'umma a Burkina faso na taimakawa da karfi da kuma makamai a rikicin kabilancin da yaki ci-yaki cinyewa a garin Bawku dake arewa maso gabashin kasar.

Hukumar 'yan sandan ta bayyana cewa, muddun ba a dauki mataki ba, to shigowar mayaka daga Burkina Faso na iya bai wa wasu 'yan ta'adda damar samun gindin zama a Ghana.

Garin Bawku a Ghana
Garin Bawku a Ghana

In kuwa ba a dau mataki ba, to shigowar mayakan daga Burkina Faso zai iya bai wa wasu yan ta'adda damar samun gindin zama a Ghana, inji hukumar 'yan sandan kasar.

Mallam Usman Muhammad Mansur, wakilin al'ummar zango a fadar sufeto janar din yan sandan kasar, ya tabbatar wa Muryar Amurka wannan bayani.

A nashi tsokacin, mai sharhi kan harkar tsaron ciki da wajen Ghana, Mallam Irbad Ibrahim, na ganin bai kamata Ghana ta alakanta rikicin kabilanci da 'yan ta'adda ba.

Muryar Amurka ta tuntubi magakujerar majalisar tsaron gundumar Bawku, Hon Hamza Amadu, wanda ya bayyana cewa, a bara wasu 'yan ta'adda na kasar Burkina Faso su ka kusanci Ghana, amma dakarun soja sun kora su kuma gwamnatinsa ta jamiyyan NPP na kokarin tsare iyakokin kasar

Bawku, dake jahar arewa maso gabashin kasar Ghana, na daga cikin garuruwa da harkokin kasuwanci ya bunkasa sosai, saboda gundumar na da iyakoki da kasashe biyu masu makwabtaka da Ghana, wato Togo da Burkina Faso.

Rikicin kabilancin na tilasa al'ummar yankin tserewa domin neman mafaka. A baya bayan nan sai da aka rufe makarantu da kasuwanni sakamakon rikicin.

Saurari cikakken rahoton Hamza Adams:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG