Hukumta mutumin da ya aikata aikin asha lokacin yake da karfin iko kamar Hissene Habre abu ne mai kyau wanda zai zama daratsi ga sauran shugabannin dake mulki yanzu.
Farfasa Bube Namaiwa na jami'ar Diof dake kasar Senegal yace komin tsawon shekaru da ya aikata aikin asha din to yi masa hulumci nada babban daratsi kuma yana da mahimmanci kwarai.
Akwai mutanen da shi Hissene Habre ya yi sanadiyar rasuwansu saboda haka yi masa hukumci zai kwantar da zuciyar 'yan uwa da sauran mutane. Hukumcin zai zama tamkar jan kunnuwan masu shirin yin abubuwan da ya yi kada su kuskura su aikatasu.
Hukumcin babban nasara ce a nahiyar Afirka cewa maimakon a kama mutum a kaishi kasar waje a yi masa hukumci yau sai gashi Afirka ta rungumi abun tana yin hukumci da kanta.
Dangane da shugabannin Afirka Farfasa Bube Namaiwa yace idan suka ji suka kuma yi nazari a kai to kafin su aikata wasu abubuwa dole ne su yi tunane domin babu wanda yayi tsammanin za'a yi irin haka a Afirka. Amma yau gashi an gurfanar da tsohon shugaban kasa saboda dimokradiya ta soma girkuwa. Mutane sun gane idan wani shugaba ya aikata aikin asha duk lokacin da ya sauka koina ya buya ana iya binsa ahukumtashi can. Ko dukiyoyin kasa mutum ya wawura ya kai ya boye lokaci na zuwa da za'a bishi koina yake a hukumtashi.
Farfasa Bube Namaiwa ya kira shugabannin Afirka su sani fa kan mage ya waye. Hatta mutanen karkara kawunansu sun waye. Ko mutum ya kashe mutane saboda yana mulki, ya yi rubdaciki da dukiyoyin kasarsa za'a cimmai kuma 'ya'yansa ba zasu ci gajiyar abun da ya sata ba.
Ga karin bayani.