AGADEZ, NIGER - Wannan mataki dai ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin al'umma musanman mata.
Hukumomin kiwon lafiya a Agadas dake arewacin Nijar sun dauki matakin bada tsaro a asibitoci domin kare lafiyar masu shigowa da kuma marasa lafiya inda hukumomin suka dauki matakin haramta sanya nikab ga mata dama wasu abubuwan dake rufe fuskokokin jama’a domin tabbatar da tsaro a cikin asibitocin.
Wannan matakin dai ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin mata inda suke bayyana ra’ayoyi mabanbanta.
Masu sharhi kan al’amuran yau da kullum sun tofa abarkacin bakinsu, kuma ganin yadda ake fuskantar matsalolin tsaro a kasar Nijar yasa suma kungiyoyin addinai suka bada goyan bayan su ga wannan matakin.
Hukumomin kiwon lafiya dai sun yi kira ga al’umma gaba daya da su basu goyan baya don su cimma burin da suka sanya a gaba a fannin tsaro.
Saurari cikakken rahoto daga Hamid Mahmud:
Dandalin Mu Tattauna