Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Nijar Sun Kona Miyagun Kwayoyi Na Milyoyin Kudade

Hukumomin Nijar A Lokacin Da Suka Kona Miyagun Kwayoyi Na Milyoyin Kudade A Jihar Agadez
Hukumomin Nijar A Lokacin Da Suka Kona Miyagun Kwayoyi Na Milyoyin Kudade A Jihar Agadez

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasar Nijar, Ocritis ta kona kayan maye na milyoyin kudade wadanda nauyinsu ya kai ton 1.5 wanda shi ne irinsa na farko a jihar Agadas da ke Arewacin Nijar.

AGADEZ, NIGER - Kayan miyagun kwayoyin da aka kona sun hada da tabar Wiwi da Cocaïne da kuma Tramadol da dai sauransu.

Miyagun Kwayoyi Na Milyoyin Kudade Da Aka Kona A Jihar Agadez, Nijar
Miyagun Kwayoyi Na Milyoyin Kudade Da Aka Kona A Jihar Agadez, Nijar

Hukumomi a jihar Agadas ta Jamhuriyar Nijar sun nuna damuwa dagane da yadda safarar miyagun kwayoyi ke nema samun gurin so sai a jihar, da kuma yadda ta’ammali da miyagun kwayoyin ke zama karfen kafa a tsaknin al’umma.

Hukumomin su ce ya zama wajibi a yi duk mai yiwuwa wajen kawo karshen wannan mummunar dabi’a domin samar da al’umma ta gari.

Hukumomin Nijar Sun Kona Miyagun Kwayoyi Na Milyoyin Kudade
Hukumomin Nijar Sun Kona Miyagun Kwayoyi Na Milyoyin Kudade

A wani na kokarin tabbatar da hakan, hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta gudanar da bikin kona kimanin tan 1.5 na kayan shaye-shaye a gaban hukumomin jihar Agadas, karkashin Henri Marthin Muktar babban alkali na jihar Agadas.

Tuni dai al’ummar garin suka bayyana jin dadinsu game da yadda ake samun nasara akan masu safarar miyagun kwayoyi.

Hukumomin Nijar Sun Kona Miyagun Kwayoyi Na Milyoyin Kudade
Hukumomin Nijar Sun Kona Miyagun Kwayoyi Na Milyoyin Kudade

Kungiyoyin farar hula sun jinjinawa jami’an tsaro bisa kokarin da suke yi, inda hukumomi suka sha alwashin baiwa hukumar duk irin goyan bayan da take bukata domin kawar da wannan mummunar dabi’a a kasa baki daya.

-Hamid Mahmud

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG