Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Jordan Sun Kubutar da 'Yan Yawon Bude Ido da Wasu 'Yanbindiga Suka Kaima Hari


Jami'an tsaron Jordan da suka kubutar da 'yan yawon bude ido jiya Lahadi
Jami'an tsaron Jordan da suka kubutar da 'yan yawon bude ido jiya Lahadi

Yanzu hukumomin kasar Jordan sun tabbatar da kubutar da 'yan yawon bude ido da suka makale a wani gini mai tarihi biyo bayan harin da wasu 'yan ta'ada suka kai wurin

Hukumomi a kasar Jordan sun ce jami’an tsaro sun samu nasarar kubutar da yan yawon shakatawa yan kasashen waje da suka makale cikin wani tsohon gini na tarihi a garin Karak, bayan hare haren da wasu ‘yan bindiga suka kai jiya Lahadi ya kashe akalla mutane goma sha hudu. Akalla kuma mutane ashirin da biyu ciki harda farar hula da kuma yan sanda aka bada rahoton cewa sun ji rauni.

Wata jaridar kasar Jordan mai suna Times ta buga labarin cewa wata baturiyar kasar Canada da akalla yan sanda guda biyar suna cikin wadanda aka kashe da wasu mutane hudu da kafofin tsaro suka ce ‘yan ta’ada ne.

Rahoton ya kuma ce an jikatta yawancin mutane ne a wani wuri na birnin, kafin yan bindigan suka kutsa tsohon gini na tarihi kila suna neman mafaka a wannan wurin mai farin jinin ‘yan yawon bude ido.

Ya zuwa daren jiya Lahadi babu kungiyar data yi ikirarin cewa ita keda alhakin kai harin kuma hukumomi basu bada wani karin bayani akan ko yan bindigan suna da alaka da kungiyoyin masu ra’ayin rikau a Syria makwapcyar kasar ba.

XS
SM
MD
LG