Sakamakon farko na zaben shugaban kasar da aka gudanar a jamhuriyar Niger na nuni da cewa, za a je zagaye na biyu tsakanin dan takarar babban jam’iyar hamayya da abokin kawancen tsohon shugaban kasar da aka hambare cikin watan Fabrairu a wani juyin mulkin soja. Bisa ga sakamakon zaben da aka sanar yau jumma’a da maraice, dadadden dan hamayya da Tanda Mahamadou Issoufou ne ke kan gaba da kashi talatin ta takwas bisa dari na kuri’un tsohon PM kuma dan takarar jam’iyar tsohon shugaban kasa Seini Oumarou kuma na biye da kashi ishirin da uku na kuri’un. Jami’an gudanar da zabe sun ce za’a yi zaben fidda gwani tsakanin Issoufou da Oumarou ranar sha biyu ga watan Maris.
Sakamakon farko na zaben shugaban kasar da aka gudanar a jamhuriyar Niger na nuni da cewa, za a je zagaye na biyu