Amurka tayi na’am da maida Niger karkashin mulkin domokaradiya, yayinda ake rantsar da Mahmadou Issoufou a matsayin shugaban kasa yau alhamis. A cikin sanarwar da ta bayar jiya Laraba, sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton tace, yanzu Mr. Issoufou yana da damar karfafa cibiyoyin damokaradiyar kasar yadda dukan mutanen kasar zasu amfana. Ta kuma taya shugaban kasar mai jiran gado murna tare da bayyana rantsar da shi a matsayin wani lokaci na tarihi da za a maida kasar karkashin turbar damokaradiya kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya tanada. Mr. Issoufou dadadden shugaban hamayya, ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar cikin watan Maris ne inda ya sami kashi hamsin da takwas bisa dari na kuri’un. A watan Fabrairu bara ne sojoji suka hambare gwamnatin Mamadou Tandja bayan ya sake kundin tsarin mulkin kasa domin kara wa’adin mulkinsa da ya cika. Muna da Karin bayani bayan labarai.
Amurka ta nuna amincewa da maida jamhuriyar Niger karkashin mulkin damokaradiya.