To sai dai wasu a Majalisa na ganin akwai abin dubawa tun da Majalisa ce ke sa ido akan ma'aikatun.
A cikin 'yan kwanaki nan ne Majalisar dattawa ta koka akan yadda ma'aikatu da hukumomin gwamnati sama da 100 suka ki bayyana a gaban kwamitin da ke kula da harkokin gwamnati na Majalisar Dattawa domin amsa tambayoyin da ake gabatarwa a rahoton babban mai binciken kudi.
Akan haka ne shugaban hukumar tattara kudade da kula da yadda ake kasafta su ga asusun gwamnati Mohammed Bello Shehu ya ce za su dauki kwararan matakai akan ma'aikatun kamar yadda doka ta tanadar masu.
Bello ya ce baya ga dukanin ma'aikatu da hukumomin gwamnati, an kara wa hukumar sa wasu hukuma guda biyar da suka hada da NNPC na da, da na yanzu, da DPR wanda yanzu ya zamu NUPRIK da CBN da Ma'aikatar Kudi, da FIRS da Hukumar Kwastan.
Ya bayyana cewa, an kawo wadanan biyar din domin su ne suke kawo kudi a asusun gwamnati.
Amma ga Sanata mai wakiltan Katsina ta tsakiya a Majalisar wakilai Ahmed Babba Kaita ya na ganin Majalisa ta na da laifi a fanin aikin ta na sa ido akan wadannan ma'aikatu.
Ahmed ya ce majalisar ta gaza a wanan bangaren.
Hukumar RMAFC a ta bakin shugaban ta, Mohammed Bello Shehu ya ce akwai mataki da hukumar ta fara dauka domin a kara wa hukumar karfi saboda ta iya ladabtar da dukan ma'aikatu da hukumomin da ba sa bin umurni.
Bello ya ce akwai bukatar a gyara dokar da ya kafa hukumar ta su, kuma tuni har sun kai bukatar haka ga majalisar dokokin kasar kuma an amince da gyaran.
Abin jira a gani shi ne ko Majalisar dokoki ta tara din nan za ta iya kammala aiki akan dokar, ko za ta bar wa Majalisa ta goma mai shigowa.
Saurari rahoton cikin sauti: