Hukumar sojin Pakistan ta shiga tsakani a takaddamar da ke tsakanin Gwamnati da 'yan adawa masu zanga-zanga, wadanda su ka taru a babban birnin kasar na tsawon makonni biyu, su na bukatar Firayim Minista Nawaz Sharif ya yi murabus.
Zakaran wasan cricket din nan da ya rikida zuwa dan siyasa Imran Khan da kuma malamin nan mai tsauri Tahir-ul-Qadri sun gana da daren jiya da Hafsan Hafsoshin soji Janar Raheel Sharif, wanda su ka amince da shi a matsayin mai shiga tsakani a wannan tattaunawar.
Da Khan da Qadri sun yi zargin cewa an tabka magudi ainon a zaben na watan Mayun 2013, wanda Sharif ya ci da gagarumin rinjaye. Masu sa ido na kasa da kasa sun ce an yi zaben cikin gaskiya da adalci. Zuwa yanzu dai Mr Sharif ya ki yin murabus. Ya yi ta kokarin warware wannan danbarwar siyasar ta wajen gudanar da jerin tarurruka da shugabannin 'yan adawar amma ba tare da nasara ba.