Hukumar samar da abinci da aikin gona ta Majalisar Dinkin Duniya tayi gargadin cewa wajibi ne Gwamnatocin kasashen nahiyar Asiya su gaggauta daukan matakan hana tashin farashin kayan abinchi da yanzu haka ke neman afkawa kasashen na Asiya,domin hana afkuwar irin abinda ya faru a shekarar 2008 da shekarar 2009.
Babban jami’in hukumar ta kula da abinchi da aikin gona yace babban matakin da ya kamata a fara dauka shine Gwamnatocin Asiya su kokarta zuba jari a aikin noma domin kara yawan kayan abinchi a kasuwanni, yace hakan zai rage yawan hauhawar da farashin kayan abinchi keyi.Yace duk da bunkasar da tattalin azrikin kasashen Asiya keyi, amma kuma gefe daya kashi sittin daga cikin dari na masu fama da matsalar yunwa miliyan dubu a duniya suna zaune ne a kasashen Asiya.
Bankin duniya yace tashin farashin abinchi ya cusa yunwa ga mutane miliyan 44 daga shekarar 2010 zuwa yau.