Rattaba hannun da shugaban kasa Muhammad Buhari ya yi akan dokar samar da ayyukan yi ya dauki hankulan matasan kasar da masu nazari akan harkokin yau da kullum.
Sun amince dokar na da mahimmanci kuma zata yi tsairi ga kasar. Dr Jibrin Ibrahim jami'i a cibiyar inganta dimokradiya ta NDI ya ce dama dokar tana cikin dokokin kasa amma ba'a aiki da ita ne. Ya ce abu na farko da dokar ta tanada shi ne idan za'a ba da kwangilar aiki a tabbatar babu kamfanin gida da zai iya aikin kafin a bayar dashi waje.
Alkalumma sun nuna cewa rashin ayyukan yi sun karu daga kashi 16 cikin dari zuwa kashi 18 cikin dan karamin lokaci.
Matasan Najeriya da rashin samun abun yi ya shafa sun bayyana ra'ayinsu dangane da dokar.
Khalid Ismail jigo a reshen matasan jam'iyyar APC ya ce akwai abubuwa da yawa da suka taso a kasar, misali shirin nan na N-Power an yi masa zagon kasa an shigar da siyasa ciki. Wadanda shugaban kasa ya nada su gudanar da shirin sun mayar dashi kafar yiwa shugaban kemfen ta hanyar sadarwar zamani. Ya ce abun ya zama siyasa ba samar wa matasa aikin yi ba.
Shi ko Abubakar Bestu ya ce matakin da shugaban kasa ya dauka abu ne da aka dade ana jira. Abun da ya sa shugaba ya rabtaba hannu a dokar saboda farfado da matasan kasar ne da masu bukatan ayyuka musamman ayyukan da suka shafi fasaha, kimiya da kuma sauran ayyukan hannu.
Abubakar Sadique Surumbai ya ce abun zai kawo matukar ci gaba musamman zai kawar da korafin da matasa su keyi na rashin aikin yi
Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.
Facebook Forum