Sana’ar sayar da shayi na cikin kananan sana’o’i masu dogon tarihi da suka dade suna bada gudunmuwa ga habbakar tattalin arzikin iyalai a kasashen nahiyar Afrika ta yamma kamar Najeriya, Nijar da makamanta su.
Sai dai a ‘yan kwanakin da suka gabata hukumar kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Najeriya wato NAFDAC ta gargadi ‘yan kasar akan su yi taka-tsan-tsan wajen amfani da shayin da ake sayarwa jama’a a bakin titunan birane da sauran garuruwan kasar, saboda zargin cewa, wasu daga cikin masu sayar da shayin na sanya wasu sinadarai da ka iya zama hadari ga lafiyar bil’adama.
Kamar sauran birane da kauyuka a yankin Afrika ta yamma, sana’ar shayi na daga cikin hanyoyin samun abinci ga mabukata cikin sauki da sauri a Kano dama sauran sassan Najeriya.
Baya ga haka, sana’ar na cikin jerin kananan harkokin kasuwanci da ke samar da kudaden bukatun yau da kullum ga dimbin masu wannan sana’a a karkara da birane.
Sai dai an dade ana zargin wasu daga cikin masu sarrafa shayi da sanya wasu sinadarai a cikin sa, wa lau na itatuwa ko wadanda bature ya sarrafa da ka iya zama illa ga jikin bil’adama.
Ta yiwu hakan ya sa hukumar kula da ingancin Abinci da Magunguna ta Najeriya ta gargadi ‘yan kasar suyi taka-tsan-tsan da masu shayi a bakin titi.
To amma Malam Nura Iliayasu, wani matashi daya shafe shekaru fiye da 15 yana sana’ar sayar da shayi daura da sinimar Plaza ta unguwar Fagge a birnin Kano ya ce duk kayayyakin shayin da suke amfani da su wanda hukuma ta amince da su ne.
Dr. Usman Mohammed na Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, yace batun tsafta shine babban abin da hukumomi ya kamata su bada himma sosai akan duk wani nau’in abinci da ‘yan kasa ke ci.
Amma Malam Nura Iyaliya ya bayyana cewa, daga cikin masu sarrafa shayi, akwai masu hade-haden itatuwa ko sinadarai da sunan karawa mutum kuzari, ko da yake ya ce ba shi da cikakkiyar masaniya game da sigar da suke bi wajen hada irin wannan shayi.
To ko hukumar NDLEA mai yaki da ababen sanya maye a Najeriya na da rawar takawa akan mutanen dake hada irin wannan shayi kuma su sayarwa Jama’a? Dr Ibrahim Abdul, shine kwamandan hukumar a jihar Kano ya ce suna iya yin amfani da sashe na 20 da 19 na dokar su da ta ce duk wanda aka kama yana hada kayan maye, za a iya gurfanar da shi ko ita gaban kuliya.
To amma Dr Usman yace akwai bukatar hukumar NAFDAC ta gudanar da sahihin bincike ta sigar ilimin kimiyya game da wannan batu, domin kaucewa yanayi na yi wa masu sana’ar shayi kudin goro.
Batun kiyaye tsaftar abinci da dai-daita nau’ukan cimaka da jikin bil’adama ke bukata shine babban ginshikin gina al’uma mai cike da koshin lafiya, kuma nauyi ne daya rataya a wuyan gwamnati da al’umar Kasa, kamar yadda masana suka sha nanatawa.
Ga karin bayani cikin sauti.