Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO ya ce yau Alhamis hukumar za ta yanke hukunci kan ko zata ayyana dokar ta baci a duniya kan cutar coronavirus.
A makon da ya gabata ne hukumar WHO ta ce barkewar annobar cutar bata kai matakin ba, amma ta bayyana hakan ne kafin adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar su kai 6,000 ba.
Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya fadawa manema labarai jiya Laraba cewa “Ci gaba da samun karuwar yaduwar cutar, da kuma shaidar tana yaduwa daga mutum zuwa mutum a wajen kasar China, tabbas abin damuwa ne matuka.
Kasashe dayawa sun kwashe ‘yan kasashensu daga Wuhan, birnin kasar China dake zaman tushen barkewar cutar. Kamfanonin jiragen sama sun dakatar da jiragensu daga zuwa China kai tsaye.
Tedros ya ce kashi 99 cikin 100 na mutanen da suka kamu da cutar 6,000 suna kasar China ne. sauran wasu kasashe 15 sun tabbbatar da kamuwar mutane 68. Ya zuwa jiya Laraba, an bayar da rahotan mutuwar mutum 132 – dukkanninsu a kasar China.
Facebook Forum