Kayan da suka hada da tabar wiwi su ne man girki da man shafawa da tufafi da tsoffin takalma da dai sauransu.
Jami'an kwastan din sun yi kamun ne a yankin Eruwa dake cikin jihar Oyo. Babban jami'in kwastan mai kula da jihohin Oyo da Osun Alhaji Abdulsalam Hassan shi ya jagoranci taron 'yan jarida domin su ga abubuwan da suka kama.
Yace sun kama kananan motoci goma sha daya ne dauke da kayan gwanjo da tabar wiwi da man girki da na shafawa. Haka ma akwai takalma kwance. Man shafawar irin na magani ne amma babu lambar hukumar NAFDAC wadda take da alhakin tabbatar da kyawon magunguna kafin a bar jama'a su yi anfani dasu.
Dangane da tabar wiwi jami'an kwastan zasu mikawa hukumar NDLEA hukumar dake yaki da fataucin miyagun kwayoyi domin ta cigaba da bincike da zummar hukunta wadanda suka aikata laifin. Sauran kayan kwastan zata rike ta yi bincike.
To saidai har yanzu hukumar bata kma kowa ba saboda wai mutanen sun tsere daji da suka hango jami'an kwastan.
Ga karin bayani.