Hukumar kwastam da ke kula da iyakokin Najeriya da na Benin, kan iyaka mafi girma tsakanin Najeriya da sauran makwabtan kasashen wato Seme, ta kama dubban buhunan shinkafa da aka so shigowa da su Najeriya ta Jamhuriyar Benin.
"Shinkafa dai sun ce ba za su bar shigowa da ita ba, mu kuma mun ce ba zamu bar kamawa ba." inji Kwanturolan kwastam mai kula da iyakar ta Seme, Abba Ali.
Ya bayyana cewa a farkon watan da ya gabata suna da shinkafa dubu goma 12 da suka kama wanda aka basu umarnin kai wa 'yan gudun hijira a sansanonin Yobe. Baya ga shinkafar kuma har da katon katon na tumatir dubu hudu da dari biyar, da jarkar mai 1000, da wasu tarkacen kaya da dama. Yanzu kuma sun yi sa'ar cafke buhunan shinkafa kusan dubu goma sha uku.
Shugaba Buhari a shafinsa na Twitter ya ce an dakile shigowa da shinkafa kasar daga Jamhuriyar Benin da kashi 90 cikin 100. Amma ana ci gaba da shigowa da shinkafar wanda hakan ke kawo cikas ga shirin gwamnati na noma shinkafar a cikin gida.
Facebook Forum