Hukumar Kiwon Lafiya Ta Duniya ta rufe daya daga cikin dakunan gwaje-gwajenta cutar abola dake kasar Saliyau, bayan da wani ma'aikacinta ya kamu da cutar .
Hukumar ta fada jiya Talata cewa ta janye ma'aikatanta da ke dakin gwaje-gwajen na Kailahun - daya daga cikin dakunan gwaje-gwaje biyu kawai dake Saliyau bayan da wani dan Senegal kwararre a fannin yaduwar cututtuka ya kamu da cutar mai saurin kisa. Wannan mataki dai zai yi mummunar illa ga yunkurin dakile yaduwar cutar da tayi tsanani fiye da yadda tayi can baya.
Ebola dai ta hallaka mutane sama da 1,400 ta kuma janyo rashin lafiya ga mutane 2,600 a Yammacin Afirka tun bayan bullarta a cikin watan Maris.