Ganin yadda wasu matsaloli ke dabaibaye aikin sufetocin gwamnati a yayin gudanar da bincike a ofisoshin ministocn gwamnatin kasar ta Nijar ya sa hukumar HALCIA kiran wani taron da ya hada jami’anta da wadannan sufetoci domin tattauna hanyoyin da za a bullo wa wannan matsala dake maida hannu agogo baya wajen yakar cin hanci da kuma farautar mahandama dukiyar jama’a. Alhaji Sallissou Oubandoma shine matemakin shugaban hukumar HALCIA.
A ci da karfafa wannan sabon mataki shugabannin hukumar sun fara hangen kafa cibiyar zuba ido da bin diddigin ayyukan bincike a kowane ofisoshin ministan gwamnatin wannan kasa.
Sufetocin sun yaba da wannan yunkuri domin a cewarsu mataki ne da zai basu damar gudanar da aiki cikin nutsuwa ba tare da wani katsalandan ba kamar yadda sufeton kasa Gounabi Adamou ya bayyana.
A watan jiya hukumar yaki da cin hanci ta bada sanarwar bankado sama da million 2000 na cfa wadanda suka makalle a hannun wasu kamfanoni da masana’antun gwamnati da masu zaman kansu wadanda suka hada da kudaden haraji da wadanda aka yi ruf da ciki a kansu.
Hukumar ta HALCIA ta lashi takobin lekawa duk inda ya dace domin karbo kudaden da aka wawure a matsayinta na mai kare dukiyar kasa daga barayin biro da abokan cuwa cuwarsu.
Saurare cikakken rahoton Sule Barma a Sauti: