Hukumar alhazan Najeriya NAHCON ta bayyana tantance kamfanonin jirgin yawo 110 don ba da damar guraben jigilar alhazai zuwa hajjin bana hijra 1445.
A sanarwa daga mataimakiyar darktan labaru ta hukumar Fatima Sanda Usara, NAHCON ta ce an duba cika wasu muhimman ka'idoji kafin amincewa da kamfanonin.
Ka'idojin sun hada da rajista da hukumar yi wa kamfanoni rajista CAC, rajistar kungiyar jigilar fasinjojin sama IATA, ingantaccen ofishi da sauran su.
Hakanan NAHCON ta ce duk kamfani sai ya gabatar da shaidar mallakar Naira miliyan 30 a ajiye a banki da kuma ba da ajiyar Naira miliyan 25 don kare muradun alhazai idan an saba musu ka'ida.
A tarihi dai a kan raba kujera dubu 10 ga kamfanonin jirgin yawo cikin kujeru dubu 95 da Saudiyya ke warewa Najeriya.
Hukumar ta alhazai ta umurci maniyyatan jihohi su ba da ajiyar Nara miliyan 4.5 zuwa karshen watan nan don hakan ya zama mizanin kidaya yawan wadanda za su iya gudanar da aikin hajjin bana.
NAHCON ta ce Saudiyya za ta fara ba da biza ta hajji mai zuwa daga farkon watan Maris amma hakan ba yana nuna sai an jira har lokacin kafin sanin yawan wadanda za su samu damar sauke faralin ba.
Dandalin Mu Tattauna