Jerin hotunan marigayi shugaba Hammani Diori na Nijar, da maidakinsa Aishatou tare da wasu shugabannin kasashen duniya lokacin mulkinsa. Da yana da rai, a wannan makon ne yake cika shekara 100 da haihuwa.
Hotunan Marigayi Hammani Diori Tare Da Wasu Shugabannin Duniya Da Matarsa Aishatou

1
Hammani Diori a kasar Jamus ta Yamma, 5 Afrilu 1968.

2
Hamani Diori, shugaban Nijar, tare da mai dakinsa Aishatou, a lokacin da shugaban Jamus ta Yamma, Heinrich Luebke (na hagu) yake tarbarsu a birnin Bonn, 19 Satumba 1968.

3
Ganawar Hamani Diori (na 4 daga hagu) da shugaba Charles De Gaulle (na uku daga hagu) na Faransa 27 Satumba 1961.

4
Diori Hamani, Shugaban Nijar a lokacin da ya je shi Nice a kasar Faransa, 26 Satumba, 1961.