Jerin hotunan marigayi shugaba Hammani Diori na Nijar, da maidakinsa Aishatou tare da wasu shugabannin kasashen duniya lokacin mulkinsa. Da yana da rai, a wannan makon ne yake cika shekara 100 da haihuwa.
Hotunan Marigayi Hammani Diori Tare Da Wasu Shugabannin Duniya Da Matarsa Aishatou

5
Hamani Diori, shugaban Nijar tare da shugaba Joseph Desire Mobutu (Mobutuy Sese Seko), a filin jirgin saman Kinshasa a kasar Kwango ranar 29 Yuni, 1968.

6
Hamani Diori, shugaban Jamhuriyar Nijar ana tarbarsa a lokacin da ya sauka a Frankfurt, Jamus ta Yamma a ranar 6 Maris, 1965.

7
Mrs. Aishatou Diori, mai dakin shugaba Hamani Diori na Nijar tare da shugaban kasar Upper Volta ()wadda ake kira Burkina Faso yanzu) Maurice Yamecco, a filin jirgin saman Rum na kasar Italiya ranar 20 Fabrairu 1965.

8
Shugaba Hamani Diori, na Nijar (dama) tare da shugaba Georgess Pompidou na Faransa, 26 Janairu 1972.