Hotunan Barnar Rokokin Boko Haram A Maiduguri.
Hotunan Barnar Rokokin Boko Haram A Maiduguri, Yuni 01, 2015
Hotunan Barnar Rokokin Boko Haram A Maiduguri.

5
Wata yarinya tana shigewa ta jikin wani gidan da ya lalace a sanadiyyar rokokin da 'yan Boko Haram suka cilla kan garin Maiduguri a ranar asabar da daddare. Ran lahadi ma, bam ya fashe a kasuwar Kwastam ya raunata mutane hudu, kwana guda bayan da bam ya tashi cikin wani Masallaci ya kashe mutane masu yawan gaske a garin na Maiduguri.

6
'Yan agaji sun hallara a kan tituna kusa da inda wani bam ya tashi ran asabar 30 Mayu, 2015 a garin Maiduguri. Wani bam ya fashe ran asabar da rana a kusa da kasuwar Kwastam ta Maiduguri, kasa da kwana guda a bayan da 'yan Boko Haram suka cilla rokoki kan garin na Maiduguri suka kashe mutane akalla 13.

7
Wani mutum yana duba wani gidan da ya lalace a sanadiyyar rokokin da 'yan Boko Haram suka cilla kan garin Maiduguri a ranar asabar da daddare. Ran lahadi ma, bam ya fashe a kasuwar Kwastam ya raunata mutane hudu, kwana guda bayan da bam ya tashi cikin wani Masallaci ya kashe mutane masu yawan gaske a garin na Maiduguri.

8
Mutane sun hallara a kan tituna kusa da inda wani bam ya tashi ran asabar 30 Mayu, 2015 a garin Maiduguri. Wani bam ya fashe ran asabar da rana a kusa da kasuwar Kwastam ta Maiduguri, kasa da kwana guda a bayan da 'yan Boko Haram suka cilla rokoki kan garin na Maiduguri suka kashe mutane akalla 13.