Kasa da mako daya a rantsar da sabuwar gwamnati a Najeriya, jama'a na kukan karancin mai saboda rashinsa a gidajen sayarwa. Wasu da dama sun dogara akan 'yan fasa kaurin man, ko bunburutu domin samun wuta da safarar jama'a. Ga kadan daga cikin hotunan wannan lamari dake faruwa a kasar da ta fi kowace kasa a nahiyar Afirka hako man fetur. Mayu 27, 2015
Karancin Man Fetur a Najeriya, Mayu 27, 2015
Jama'ar Najeriya na fama da matsalar rashin mai, saboda yajin aikin ma'aikatan man fetur wanda aka kawo karshensa a baya-bayannan. Sai da ya zuwa yanzu, babu mai a gidajen mai.

1
Masu motocin haya sun tsaya cak sakamakon rashin man fetur da 'yan Najeriya ke fama da shi. Mayu 27, 2015

2
Jami'an Tsaro a Najeriya na gardama da masu sayan man fetur. Mayu 27, 2015

3
Jama'a da dama sun dogara akan 'yan fasa kaurin man fetur domin samun wutar lantarki. Mayu 27, 2015

4
Harkokin bunburutu na bunkasa a dai-dai wannan lokaci da Najeriya ke fuskantar karancin man fetur. Mayu 27, 2015