Wani kakakinta ya bayyana janye yakin neman zaben, wanda aka tsara zai kunshi bude gidauniyar neman kudaden yakin neman zabe, da kuma wani jawabi da aka shirya za ta yi kan tattalin arziki.
Gangamin yakin neman zaben na Clinton, ya bayyana cewa wani likiti ya duba ta tun a ranar Juma’a, bayan da ta yi ta fama da tari, inda a lokacin ne kuma aka fada mata cewa tana fama da cutar ta Pneumonia.
A lokacin ne kuma, likitoci suka ba ta wasu magunguna kashe kwayar cutar, suka kuma ba ta shawarar ta dauki hutu, tare da sauya tsarin yadda ta ke tafiyar da ayyukanta.
Amma sai a ranar Lahadi aka bayyana wannan matsala da Clinton ke ciki, bayan da jikinta ya tashi a wajen taron bikin tunawa da harin da aka kawo nan Amurka na ranar 11 ga watan satumba a shekarar 2001.
Nan take ne kuma ta fice daga wurin taron, inda wani hoton bidiyo ya nuna yadda wasu suka tallafe ta, suka kuma taimaka mata ta shiga mota.
Daga bisa ni dai, an ga Clinton, mai shekaru 68, ta leko daga gidan ‘yar ta Chelsea da ke birnin New York, inda ta dagawa magoya bayan ta hanu tana cewa ta samu sauki.