A ci gaba da shirinmu na Ramadana, a yau DandalinVOA ya ziyarci wata Kungiya mai tallafawa mata wadanda aka ci zarafinsu, marayu da 'yan mata inda ya zanta da shugabar kungiyar Barrista Sadiya Adamu Aliyu, wacce suka yi rabon kayan sallah ga marayu ganin karatowar Sallah karama.
Ta ce suna ba da wannan tallafi ne domin taimakawa marasa karfi ganin wannan wata lokaci ne na taimakawa mabukata da kayan masarufi da kuma kaya domin samun rahamar ubangiji.
Barrista Sadiya Adamu Aliyu, ta kara da cewa, daga cikin wadanda aka bai wa tallafin, an taimakawa wasu daga cikin wadanda suka dan tasa wato suka girma wajen ganin kamata ya yi a koya musu sana’a domin su zamo masu dogaro da kai.
Sannan ta kara da, cewa suna sa ran koya musu wannan sana’a ce bayan Sallah domin ko da bayan Sallah ba sai an zaunar da su ana ba su kayan masarufi ba.
Amma da zarar suna da sana o'o'in hannu idan shekara ta zagayo sai dai su ma su taimakawa wasu na kasa da su.
A saurari cikakken hirar su daga rohoton Baraka Bashir
Facebook Forum