Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hauhawar Farashin Kayayyaki A Najeriya Yafi Na Shekaru 17 Baya Muni


'yan kasuwa sun yi gangami a kano
'yan kasuwa sun yi gangami a kano

Hukumar Kididdiga ta Najeriya ta fitar da bayaniai da ke nuni da cewa, hauhawar farashin kayayyaki a kasar ya karu zuwa kashi 19.64% lamarin da ke zama mafi girma da muni da aka taba samu a kasar tun shekarar 2005 .

Wannan dai na nuni da cewa matsin rayuwa da al’ummar Najeriya ke fuskanta ya dada muni la’akari da canjin da aka samu na hauhawar farashin kayayyaki musamman na masarufi wanda suka rubanya na shekarun baya da suka gabata

An samu kari a hauhawar farashin kayayyakin abinci, daga kashi 20.60 cikin 100 a watan Yuni zuwa kashi 22.02 a watan Yuli, wanda ake ganin ya samo asali ne sakamakon hauhawar farashin biredi da hatsi, da sauran kayayyakin abinci

Alkalumar farashin kayayyakin masarufi na hukumar kiddiga ta Najeriya a watan yulin shekarar 2022 da muke ciki ya yi nuni da cewa an samu karuwar kashi 18.17 cikin 100 wato sama da kashi 18.62 cikin 100 da aka samu a watan Yuni da ya gabata a shekarar lamarin da ke nuni da cewa an samu sauyin farashi a ayyuka da kayyakin da mutane ke amfani da su na yau da kullun batun da masanin tattalin arzikin kasa a Najeriya Dakta Isa Abdullahi ya ce hakan ba karamin shafar tattalin arzikin kasar zai yi ba, ta fannin tsare tsare.

A nashi bangaren, mai sharhi kan al’amuran yau da kullum a kasar Hassan Sardauna cewa ya yi dole al’umma su yi wa kasar adalci domin hauhawar farashin kayayyaki ya shafi kasashe da dama a fadin duniya.

Rahoton dai ya bayyana cewa an samu kari mai yawa a farashin kudin siyan iskar gas, man fetir da dizal da jigilar fasinjojin jiragen sama, tufafi, da dai sauransu

Saurari cikakken rahoton Ibrahim cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG